Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta sake barazanar tafiya yajin aiki muddin gwamnatin tarayya ba ta janye tuhumar da take yi mata a gaban kotu ba.

Gwamnatin tarayyar ta shigar da ƙorafinta gaban kotu tare da neman hana ƙungiyar tafiya yajin aiki tun a yunƙurin farko da ƙungiyar ta yi na tafiya a baya.
Shugaban ƙungiyar Jor Ajaero ne ya sanar da hakan yau a Abuja bayan da ƙungiyar ta yi wani zama na majalisar zartarwa.

Ƙungiyar ta baiwa gwamnatin mako guda don janye ƙarar da ta shigar gaban kotun ko kuma su tafi yajin aikin gama gari a ranar 14 ga watan Agustan da mu ke ciki.

Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙungiyar ƙwadago da ƴan kasuwa ƙara a gaban kotu tare da ayyana yajin aikin da za su tafi a matsayin haramtacce.
Hakan ya sa kotu a farko ta dakatar da ƙungiyar daga tafoya yajin aikin da ta ƙudiri aniyar tafiya.
A ranar Laraba ne ƙungiyar ta yi yajin aiki tare da zanga-zanga wanda hakan ya sa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin tare da cimma matsaya, kuma hakan ya sa ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin a jiya Alhamis.