Shugaban ƙasar Amuruka Joe Biden ya bayyana aniyar ƙasar na goyon bayan mulkin farar hula tare da yin duk mai yuwuwa wajen tabbatar da mulkin demokaraɗiyya a jamhuriyar Nijar.

Sannan shugaban ya yi kira da a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ƙasar Nijar Mohammed Bazoum tare da gagaguta mayar da muki ga hannun farar hula.

Shugaban ya yi kiran ne a ranar Juma’a a jawabin da yayi yayin da ƙasar Nijar ke cika shekara 63 da samun ƴancin kai.

Shugaba Joe Biden ya ce za su goyi bayan ƴan ƙasar Nijar na ganin wanda su ka zaɓa ya ci gaba da mulkin ƙasar kamar yadda aka zaɓeshi.

Sannan ƙasar na yi Ala-wadai da juyin mulki da aka yi a jamhuriyar Nijar, wanda ya alaƙata hakan da tauye demokaraɗiyya.
Idan ba a manta ba shugaban mulkin soja na ƙasar Nijar kuma jagoran juyion mulkin Janar Abdourahmmane Tchiani ya gargaɗi ƙasashen ƙetare wajen shiga tsakani domin taimakawa don ƙwace mulki daga hannunsu.Shugaban ƙasar Amuruka Joe Biden ya bayyana aniyar ƙasar na goyon bayan mulkin farar hula tare da yin duk mai yuwuwa wajen tabbatar da mulkin demokaraɗiyya a jamhuriyar Nijar.

Sannan shugaban ya yi kira da a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ƙasar Nijar Mohammed Bazoum tare da gagaguta mayar da muki ga hannun farar hula.

Shugaban ya yi kiran ne a ranar Juma’a a jawabin da yayi yayin da ƙasar Nijar ke cika shekara 63 da samun ƴancin kai.

Shugaba Joe Biden ya ce za su goyi bayan ƴan ƙasar Nijar na ganin wanda su ka zaɓa ya ci gaba da mulkin ƙasar kamar yadda aka zaɓeshi.

Sannan ƙasar na yi Ala-wadai da juyin mulki da aka yi a jamhuriyar Nijar, wanda ya alaƙata hakan da tauye demokaraɗiyya.

Idan ba a manta ba shugaban mulkin soja na ƙasar Nijar kuma jagoran juyion mulkin Janar Abdourahmmane Tchiani ya gargaɗi ƙasashen ƙetare wajen shiga tsakani domin taimakawa don ƙwace mulki daga hannunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: