Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka mutane 17 a cikin karamar hukumar Barkin Ladi da ke Jihar Filato.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an kai harin ne a garin Heipang da ke karamar hukumar a daren Laraba da zuwa wayewar yau Alhamis.
Wani mazaunin kauyen na Heipang mai suna Julius Pam wanda harin ya rutsa da ‘yan uwansa shine ya shaidawa manema labarai faruwar lamarin.

Julius ya ce ‘yan bindigan sun shiga yankin ne da asubahin ranar Alhamis, inda suka hallaka mutane 17 ciki har da dan uwansa matarsa da kuma yaransu.

Wata majiya daga ofishin rundunar ‘yan sandan Jihar ta tabbatar da cewa tuni aka tura jami’an ‘yan sanda yankin da lamarin ya faru.
Harin na zuwa ne bayan da gwamnatin Jihar ta kaddamar da wata cibiyar tattara bayanai ta tsaro domin bai’wa mutanen Jihar damar sanar da jami’an tsaro halin da ke faruwa a yankunansu.
