Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata kisan kai tare da wani fasinja daya a Jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Omolola Odutola ce ta tabbatar da hakan ga manema labarai a Abeokuta a ranar Laraba.

Ta ce an kama mutanen ne a ranar Lahadi a kan titin Papalanto da ke hanyar Legas zuwa Abeokuta.

Kakakin ta ce an samu mutanen ne tare da wata karamar bindiga kirar gida cike da harsashi a cikin ta.

Jami’ar ta ce jami’an nasu sun kama mutanen ne a lokacin da su ke gudanar da sintiri a kan hanyar, inda su ke haye kan babur mara lamba.

Omolola ta ce a lokacin da mutanen su ka je dab da ‘yan sandan sai aka tsayar dasu su kaki tsayawa, inda suka yi kokarin guduwa hakan ya sanya aka bi su harta kai ga an kamasu da wani fasinja daya.

Odutola ta bayyana cewa a lokacin da ake kokarin kama mutanen daya daga cikin su ya ciji dan sanda a yatsansa.

Kazalika ta ce nan bada dadewa ba za a gurfanar da mutanen a gaban kotu domin yi musu hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: