Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa a Najeriya sun samar da janye yajin aikin da su ka shafe kwanaki 17 su na yi.

Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne a yau Asabar bayan wata ganawa da gwamnatin tarayya.


Daga cikin abubuwan da su ka tattauna kuma gwamnatin ta amince da shi har da kafa gidauniyar horaswar likitocin da za a kafa.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa Dakta Orji Emeka ya tabbatar da cewa kafa gidauniyar na sahun gama cikin jerin bukatun da su ke nema daga wajen gwamnatin.
Likitocin dai sun ce za su zauna tare da duba cigaban da aka samu daga gwamnatin zuwa makonni biyu domin duba matsaya a kai.
Daga cikin dalilan da su ka neman har da inganta albashi da tsarin kulawa da aikinsu.
Likitocin kashi 60 ne cikin ɗari da su ka kauracewa asibitoci da nufin yajin aiki.
A makon da ya gabata gwamnatin tarayya ta aikewa hukumar kula da kudi da kasa don dakatar da albashin likitocin.