Malaman addinin musulunci a Nigeria sun isa jamhuriyar Nijar domin shiga tsakani kan batun juyin mulki da aka yi a ƙasar.

 

Tuni su ka fara tattaunawa da sojojin ƙasar dangane da batun juyin mulki da aka yi.

 

Ƙungiyar malaman karkashin jagorancin Sheik Bala Lau sun isa Nijar da nufin tattaunawa da sojojin sa su ka yi juyin mulki.

 

Daga cikin malaman da su ka isa ƙasar akwai Sheik Bala Lau da ya jagoranci tawagar, sai Sheik Karibullah Sheik Muhammad Nasiru Kabara, da Farfesa Mansur Sokoto.

 

Tawagar malaman sun gana daa shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja dangane da batun juyin mulki a Nijar.

 

Sai dai daga bisan ƙungiya ECOWAS ta umarci jami’an tsaronta da su kasance cikin shiri don abkawa kasar Nijar da yaƙi da nufin kwato mulki.

 

Batun da malaman su ka shawarci shugaban da a dakatar da ɗaukar matakin.

 

Ƙungiyar ECOWAS dai ta lashi takobin kwato mulki daga hannun sojin Nijar don dorewar demokradiyya a kasar.

 

Malaman da su ka isa Nijar a yau za su gana ne da sojojin da su ka yi juyin mulki don shiga tsakani tare da samar da masalaha a kai.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: