Dandazon mutane a jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga a yau da nufin kin amincewa da matakin kungiyar ECOWAS na amfani da karfin soji a ƙasar Nijar.

Mutanen sun fito ne tare da nuna goyon baayaan sulhu do sojin da ke mulki maimakon abkawa ƙasar da yaƙi.


Masu zanga-zangar dai na nuni da cewar Najeriya da Nijar abu ne guda kuma yan uwan juna don hakaa bai kyautu a abka musu da yaki ba.
Zanga-zangar na zuwa ne bayan da kungiyar ECOWAS ta umarci dakarunta daa su kasance cikin shirin ko ta kwana a kna batun kwato mulki daga hannun sojin Nijar.
Masu zanga-zangar dai sun nuna rashin gamsuwa dangane da matakin ƙungiiyar ECOWAS.
Jami’an soji a Nijar sun yi juyin mulki tare da karbe iko daaga hannun hambararren shugaban kasar Mohammed Bazoum.
Tuni su ka cigaba da rabon muƙamai a mataki daban-daban tare da gargadi ga kasashen da ke son shiga don kwace mulkin daga hannunsu.
