Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya ce ba shi da niyyar ƙara farashin litar man a halin da ake ciki.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar bayan da aka fara yaɗa batun yuwuwar ƙara farashin litar man zuwa naira 750 daga naira 617 da ake siyarwa a yanzu.

Ƙarin farashin man na da alaƙa da tashin farashin dala da ake siyarwa naira 950 a kasuwar bayan fage.

Sai dai kamfanin ya ce ba shi da niyyar ƙara farashin man a halin yanzu.

Sannan zai ci gaba da siyar da man aa farashin 617 kan kowacce lita a gidajen man da ke Najeriya.

Farashin litar mai dai ta koma naira 617 ne bayan da aka cire tallafin man kamar yadda shiga Bola Ahmed Tinubu ya bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: