Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani malamin addinin Musulunci mai suna Malam Abubakar Mushawy Ibrahim tare da matarsa da yaransu biyu a Jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa daga cikin ‘ya’yan malamin da aka yi garkuwa da su ciki harda jariri dan kwana daya da haihuwa a lokacin da aka yi garkuwa da su a ranar Laraba da ta gabata.

Maharan sun shiga gidan malamin ne a kauyen Fondisho da ke kan hanyar babban titin Kaduna zuwa garin Zariya.

Wasu majiyoyi a yankin sun bayyana cewa an yi garkuwa da mutanen kwana daya bayan matar malamin ta haihu.

Majiyar ta kara da cewa ‘yan uwan mutanen da abun ya rutsa da su basu da hali domin sun gaza hada naira miliyan 20 kudin fansar da ‘yan bindigar su ka nema daga wajensu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: