Wasu ‘yan bindiga a Jihar Edo sun hallaka Peace Chinyereugo matar wani Fasto mai suna Samuel Chinyereugo a Jihar.

‘Yan bindigar sun hallaka matar ne a ranar Litinin a harabar Cocin da misalin karfe 7:36 na dare.
Rahotanni sun bayyana cewa an harbe matar Faston bayan dawowar su daga kai ziyara gidan wani abokinsa, inda ‘yan bindigar suka bisu har cikin cocin su ka hallaka ta.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar guda uku sun fito daga cikin motarsu sannan suka budewa faston da matarsa da kuma wani hadiminsa wuta.

Shaidun sun ce bayan ‘yan bindigar sun tafi aka kwashe su zuwa wani asibiti, inda likitoci su ka tabbatar da mutuwar matar faston.
Kakakin rundunar yan sandan Jihar Edo SP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa rundunar su ta fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka yi aika-aikar.