Dan Majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kananan hukumomin Musawa da Matazu a Jihar Katsina Hon Abdullahi Aliyu Talban Musawa ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya tura karin jami’an soji Jihar ta Katsina domin magance matsalolin tsaro da Jihar ke fuskanta.

Abdullahi ya bayyana hakan ne bayan wata zanga-zanga da mutanen da yake wakilta suka yi sakamakon yin garkuwa da wasu manoma da ‘yan bindiga su ka yi a Jihar.
Aliyu ya bayyana cewa kaiwa Jihar karin sojoji zai taimaka matuka wajen magance matsalar tsaro a Jihar.

Hon Aliyu ya kara da cewa sugaban Tinubu da dukkan wani mai ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro a Kasa suna da gudummawar da za su iya takawa wajen magance matsalolin da manoma ke fuskanta a halin yanzu.

Kazalika ya ce a halin yanzu matakan da ake dauka a fannin tsaro a yanzu ba zai wadatar ba matukar ba a kara inganta sha’anin tsaron ba.
Hon Abdullahi Aliyu ya bayyana cewa dole a kaiwa masu karamin karfi dauki bisa tabarbarewar tattalin arzikin su na yau da kullum, sakamakon gujewa yin noma da kasuwanci ganin yadda ‘yan bindiga su ka addabe su.