Kungiyar mayakan ISWAP ta aike da wata gayyata ga takwararta ta Boko Haram zuwa filin daga domin su yi musayar wuta a tsakaninsu.

Mai sharhi akan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zogazola Makama ne ya bayyana hakan ta cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a.
Zagazola ya bayyana cewa ISWAP ta zargi Boko Haram da batar da mutane, aikata karya suna boye gaskiya aikata rashawa da kuma yi wa mata fyade da sunan bautar Allah.

Zogazola ya ce bayan aikewa da boko haram gayyata da ISWAP ta yi, ta amsa gayyatar, inda su ka gwabza fada a kauyen Gaizuwa da ke Jihar Borno.

Masanin ya kara da cewa a yayin fadan sun kashe junansu da dama.
Ya ce anan gaba kungiyoyin za su sake yin wani fadan nan da wata biyu masu zuwa akan yadda boko haram ta kwashe ISWAP mutanen ta tare da hallaka su.