GwamnaJihar Yobe Mai Mala Buni ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 20 a Jihar.

Gwamnan ya rantsar da sabbin kwamishinonin ne a ranar Asabar.
A yayin jawabinsa ya bukaci da kwamishinonin su tsaya tsayin daka wajen ganin an yiwa al’umma ayyukan da su ke bukata

Gwamnan yayi kira ga Kwamishinonin da su kara kaimi wajen sauke nauyin da aka dora musu.

Daga karshe gwamnan ya ta ya su murna bisa nasarar zamowar su kwamishinoni a Jihar.