Sabon ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya sha alwashin rushe dukkan gine-gine da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.

Wike wanda ya bayyana haka a jawabinsa na farko bayan shigarsa ofishinsa a yau Litinin.

Ya bayyana damuwarsa a kan yadda ake samun ƙaruwar rashin tsaro a birnin tarayya Abuja.

A yayin jawabinsa da yake ganawa da ƴan jarida bayan shan rantsuwa, Wike ya gargaɗi dukkan waɗanda su ka yi gini a wuraren da bai dace ba da su tabbatar da cewar zai rushe shi.

Sannan ya ce za su tabbatar sun karɓe filayen da aka mallakawa wasu kuma ba su gina ba domin baiwa waɗanda su ka shirya ginawa.

Sabon ministan ya sha alwashin tsaftace harkar gine-gine tare da rushe waɗa da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.

A yau Litinin ministan ya kama aiki bayan shan rantsuwa daga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: