Majalisar dokoki a jihar Legas ta dakatar da kwamishinoni 17 da gwamnan ya aike mata domin tantancewa.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo Olu  dai ya aike da sunayen kwamishinoni 39 kuma majalisar dokokin jihar ta yi watsi da sunayen mutane 17 daga ciki.

Mafi yawan kwamishinonin da aka dakatar su ne waɗanda su ka yi aiki da gwamnan
tun a zangon mulkinsa na farko.

Wasu daga cikin kwamishinonin da aka dakatar sun haɗa da tsohon kwamishinan ilimi, lafiya, ayyuka da kuma tsohuwar kwamishiniyar al’amuran mata.

Gwamnan ya aike da sunayen kwamishinonin ne a zauren majalisar dokokin jihar, domin amincewarsu da kuma sahale masa naɗasu don taimaka masa a mulkinsa.

Babajide Sanwo Olu ya fara mulkin jihar a karo na biyu, bayan day a kamala wa’adinsa na farko karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: