Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta na cigaba da ƙoƙari wajen ganin a daƙile aikin shigo da dataccen mai daga waje.

Daga cikin ƙoƙarin da ta ce ta na yi har da tabbatar da dawo da matatun man fetur da gas na faɗin ƙasar yadda za a kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya.
Ƙaramin ministan albakatun man fetur na ƙasar Sanata Heineken Lokpobiri ne ya bayyana haka bayan ziyartar matatar man fetur da ke Fatakwal ranar Alhamis.

A cikin jawabin ya tabbatarwa da ƴan Najeriya cewar matatar mai ta Fatakwal za ta koma aiki kafin ƙarshen shekarar 2023 da mu ke ciki.

Sannan za ta kasance cikin aikin tace mai ganga dubu 50 zuwa dubu 60 a kowacce rana.
Ya ƙara da cewar za su koma aikin gayarn matatun man Warri da kuma Kaduna domin ganin an kawo ƙarshen shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.
A na sa ran matatar mai ta Warri za ta koma aiki daga watan Fabrairun shekara mai zuwa wanda za a dinga samar da ganga dubu 60 zuwa 70 a kowacce rana..