Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina sun samu nasarar kuɓutar da wani Hashim Yusif mai shekaru 65 a duniya bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da shi.

An yi garkuwa da mutumin a garin Hayin Gada da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Abubakar Saddiƙ ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar.

Ya ce a daren Alhamis wayewar Juma’a su ka samu labari kuma nan da nan su ka yi ƙoƙarin haɗa kan jami’an su don kuɓutar da wanda aka yi garkuwa da shi.

Sai dai ya ce an yi musayar wuta tsakanin ƴan sandan da ƴan bindigan kafin kaiwa ga nasarar kuɓutar da mutumin.
A jawabinsa ya ce sun samu labarin yin garkuwa da mutumin ne a daren Juma’a sannan su ka samu nasarar daƙile harin yayin da su ka kuɓutar da dabbobi bayanmusayar wuta.
Kuma da yawa sun gudu ɗauke da raunin harbi a jikinsu.
Kwamishinan ƴan sandan jihar ya yabawa jami’ansu, sannan sun buƙaci a gaggauta sanar da su yayin da aka ga wani ɗauke da raunin harbi a jikinsa.