Hukumar tsaron fararen hula a Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu matasa 20 da ake zargi da satar kayan gwamnati.

Kwamandan hukumar a Abuja Olusola Odumosu ne ya bayyana haka ya ce mutanen da aka kama an samesu da lalata kadarorin gwamnati da kuma yin sata.
Y ce hukumar ba za ta lamunci lalata ko satar kayan gwamnati ba, hakan ya sa su ka fito da sabbin dabaru don daƙile hakan.

Daga ciikin dabarun da su ka ƙara akwai sintirin cikin dare da jami’ansu ke yi kuma a yayin sintirin su ka kama waɗanda ake zargi.

Ya ƙara da cewa waɗanda aka kama su na hannunsu domin cigaba da bincike, sannan za su miƙasu ga hukumar bai wa muhalli kariya a Abuja domin gurfanar da su a gaban kotu.
Sannan kwamandan ya gargaɗi masu irin wannan ɗabi’a da su tuba domin a yanzu za su cigaba da farautarsu ba dare ba rana.
