Shugaban Najeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS Bola Tinubu ya shawarci sojojin da ke mulki a jamhuriyar Nijar da su miƙa mulki cikin watanni Tara.

Tinubu na wannan kira ne yayin da ya karbi tawagar koli ta addinin musulunci karkashin mai alfarma Sarkin Musulmi.
Tinubu ya roki sarkin Musulmin a kan kada su gaza da su sake komawa Nijar tare da rokon sojojin su mika mulki cikin watanni Tara.

Ya ce idan aka yi hakan an kwatanta da lokacin da aka yi juyin mulki a Najeriya a shekarar 1990 kuma aka samu nasara.

Ya ce muddin sojojin da gaske su ke za su aikata haka cikin watanni Tara.
Tinubu ya ce matuƙar su ka amince da haka za a gaggauta sassauta takunkumin da aka kakabawa Nijar ganin yadda ake shan wahala.
A wani labarin kuma sojojin Nijar sun bukaci a gaggauta fitar da jakadan Faransa daga kasar.
Umarnin na zuwa ne bayan da su ka aike da takarda domin ganin ya fita daga Nijar.