An sami tashin hankali a ƙauyen Birnin Magaji a jihar Zamfara, bayan wani basarake ya tilasta matasan da suka cafke matan ƴan bindiga sun sakesu.

Matasan dai sun kama matan ƴan bindigan ne sannan suka sha alwashin cewa ba za su sake su ba, har sai sun sako musu mutum shida da suka sace a ƙauyen.


Gwamnatin jihar ta nuna takaicinta kan sakin matan Fulanin guda biyu, inda ta nesanta kanta daga lamarin sannan ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike a kai.
Duk da cewa manema labarai ba su samu jin ta bakin basaraken ba, Alhaji Ussaini Magaji, sakatarensa ya bayyana cewa za su yi magana kan lamarin a lokacin da ya dace.
Wani kwamishina a jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Birnin Magaji ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne cewa gwamnatin jihar ta bayar da umarnin a saki matan ƴan bindigan kamar yadda ake yayatawa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ba ta da masaniya cewa an kama matasan da suka riƙe matan Fulanin, inda ya ƙara da cewa za a gudanar da bincike.
Rahotannin sun bayyana cewa bayan basaraken ya bayar da umarnin sakin matan, an ɗauke su akan babura zuwa wani daji domin komawa wajen mazajensu.
Sakin matan dai ya janyo tashin hankali da sanya shakku musamman a zukatan ƴan uwan mutum shidan da aka sace waɗanda har yanzu suna hannun ƴan bindiga.