Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya sauke jakadan Najeriya a ƙasar Burtaniya (UƘ), Sarafa Isola, sannan ya umarci ya dawo gida Najeriya,

Sanarwar kiran dawo da jakadan na kunshe ne a cikin wata wasika mai ɗauke da sa hannun Yusuf Tuggar, ministan harkokin waje, da kwanan watan 31 ga watan Agusta, 2023.
Ministan ya ce yana farin cikin sanar da shi matakin da shugaban kasa ya dauka na kiran sa ya dawo gida, wanda ke nuna karshen wa’adinsa na jakadan Tarayyar Najeriya a kasar Birtaniya ya kare.

Bayan wannan saƙo, yanzu ana sa ran zai fara shirin miƙa mulki, kuma ya ɗauki hutu a hukumance na kwanaki 60, sannan ya dawo Najeriya nan da ranar 31 ga Oktoba, 2023.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya naɗa Mista Isola a matsayin babban jakadan Najeriya a kasar Birtaniya a watan Janairu, na shekarar 2021.
Haka kuma a baya Isola ya taba rike mukamin ministan ma’adinai da karafa a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban kasa, Alhaji Umaru Musa Yar’Adua.
Wannan mataki na zuwa ne awanni kaɗan bayan shugaba Tinubu ya tsige shugaban hukumar NASENI ta tarayya, inda ya maye gurbinsa da matashi ɗan shekara 32 a duniya.