Bayanai sun fito a game da yadda za ayi rabon Naira Tirilyan 3.8 da gwamnatin Najeriya ta samu daga haraji.

Gwamnatocin jihohi da kuma gwamnatin tarayya su ne za su tashi da kaso mafi tsoka.
Adadin abin da za a raba shi ne Naira tiriliyan 3 da biliyan 860 da miliyan 867 da dubu 322 da 987 da digo 42 inda gwamnonin Najeriya kadai za su karbi 73% na kudin shigan da aka tara.

Gwamnatin tarayya za ta samu kashi 14% daga cikin kudin yayin da hukumar tattara haraji ta kasa FIRS mai alhakin tattara haraji a kasar nan za ta samu 4%.

Kwararrun da su ka yi sanadiyyar samun kudin su na da 5% na Naira tiriliyan 5%, amma ba za a sake biyansu a cikin kason ba.
Rahoton ya ce lauyoyin gwammatin tarayya su na da 2% yayin da bankuna da wasu za su samu 2% da za a biya sau daya a tashin farko.
Gwamnatocin tarayya da na jihohi za su cigaba da karbar kudin a duk lokacin da aka tara harajin da ya jawo aka shigar da kara a kotu.