Kwamitin zartaswa na kasa a jam’iyyar NNPP sun kori tsohon dan takarar shugabancin kasar jam’iyyar Sanata Rabiu Kwankwaso, biyo bayan kin bayyana da yayi a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.

Idan za a iya tunawa shugabanvin jam’iyyar ya dakatar da Kwankwason, a taron jam’iyyar na kasa da ya wakana ranar 29 ga watan Ogustan da ya gabata a birnin Legas.

Babban kwamitin zartarwar jam’iyyar sun nada kwamitin ladabtarwa da zasu gayyaci tsohon gwamnan domin ya kare kansa, bisa tuhumar cin amanar jam’iyya da kuma wadaka da kudin yakin neman zaben jam’iyya cikin kwanaki biyar.

Kwamitin kuma yayi gargadin cewa gaza bayyana gaban kwamitin zai janyo korar Sanata Kwankwason daga jam’iyyar, bisa la’akari da tanadin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2022 ya yi.

Saboda haka, mai rikon kwaryar sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Abdulsalam Abdulrasaq ya bayyana a cikin wani jawabi a yau Talata a birnin Legas cewa, kwamitin zartarwar jam’iyyar sun kori Kwankwason nan take, saboda kin girmama gayyatar kwamitin ladabtarwar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Abdulsalam Abdulrasaq yana sanar da hukuncin da suka dauka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: