Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi manyan nade-nade a gwamnatinsa a jiya Talata 5 ga watan Satumba.

Wadannan sabbin nade-nade an yi su ne a ma’aikatar gudanarwa ta Birnin Tarayya (FCTA).


Fadar shugaban kasar ce ta bayyana haka a jiya Talata 5 ga watan Satumba a shafin Twitter.
Tinubu ya yi wannan nadin a ranar da ya cika kwanaki 100 a kan karagar mulki tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.
Wannan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan shugaban ya tafi Indiya don halartar taron G-20 bayan gayyatar Fira Ministan Indiya, Narendra Modi.
Sabbin nade-naden guda takwas sun hada da, 1. Bitrus L. Garki – Sakataren gudanarwa na birnin Tarayya 2. Lawan Kolo Geidam – Sakataren Noma da raya karkara 3. Danlami Ihayyo – Sakataren ilimi 4.Adedolapo A. Fasawe – Sakataren lafiya 5. Salman Dako – Sakataren bangaren shari’a 6. Chinedum Elechi – Sakataren tattalin arziki da tsare-tsare 7. Uboku Tom Nyah – Sakataren sufuri. 8 Muntari Abdulkadir – Sakataren ci gaban al’umma.