Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya yabawa wani mai suna Yusuf Sulaiman Abdullahi bisa dawowa da gwamnati albashin da aka turawa mahaifinnsa bayan rasuwarsa.

 

Yabon ya fito ne ta hannun mai magana da yawun gwamnatin kan kafafen sadarwa na zamani inda ya wallafa a shafinsa.

Shi dai mahaifin wanda ya mayar da kuɗin ya rasu tun cikin watan Agustan shekarar da ta gabata, sai dai gwamnati ta cigaba da biyansa albashi har zuwa watan Agusta na shekarar da muke ciki.

Daga bisani bayan tabbatar da rasuwar mamacin dan nasa ya dawo da kudi kimanin naira 328,115 zuwa asusun gwamnati kuma ya sanar da gwamnatin cewa mahaifin nasa ya rasu kimanin shekara guda da ta gabata.

 

Mai magana da yawun gwamna ya ce gwamna ya yabawa Yusuf bisa wannan namijin kokari.

Sannan ya yi kira ga matasa masu tasowa akan su yi koyi da wannan abin kirki.

 

Akan halin kwarai da wannan bawan Allah ya nuna ya ja masa yabo daga bangarorin al’umma daban-daban, in da gwamna da kansa ya gayyaceshi suka gana tare da yi masa godiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: