Kotun Koli da ke ƙasar Faransa ta yanke hukunci kan karar da kungiyar Musulmai ta shigar kan dokar hana sanya Abaya ga dalibai.

 

Amma kungiyoyin Musulmai na Action for the Rights of Muslim da Council of the Muslim Faith sun shigar da kara don kalubalantar dokar.

 

Sai dai kotun ta tabbatar da sabuwar dokar da gwamnatin ta saka na haramtawa mata Musulmi sanya abaya a manyan makarantu.

 

Idan ba a manta ba Faransa ta kafa dokar ne don raba al’amuran hukumomi da addini.

 

A cewarta dokar za ta hana fayyace wane addini mutum ya ke a makaranta wanda zai taimaka wurin rage cin zarafin dan Adam.

 

Ta kara da cewa kungiyoyin Musulmai da sauran daidaikun mutane sun soki wannan doka da cewa cin zarafi ne.

 

Da kotun ke yanke hukunci, ta ce ba za ta iya amincewa da bukatarsu ba don haka ta tabbatar da dokar.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: