Gamayyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya sun buƙaci jami’an soji da su gaggauta hallaka ƴan ta’addan da su ka ki mika wuya.

Shugaban gwamnonin Babagana Umara Zulum ne ya buƙaci hakan a madadin sauran gwamnonin yau Asabar.

Yayin taron tattaunawa da ƙungiyar ta yi karo na Takwas, gwamnonin sun buƙaci sojin da su tabbatar da zama lafiya a yankin.

Gwamnonin sun yabawa jami’an soji bisa ƙoƙarin da su ke na wanzar da zaman lafiya.
Gwamnonin sun buƙaci dawo da zaman lafiya a yankin.
Arewa maso gabashin Najeriya na fama da matsalar tsaro ta Boko Haram, da sauran muggan ayyuka.
Idan ba a manta ba sojin sun ce sun samu nasarar hallaka sama da yan ta’adda 800 cikin watanni uku.