Wata kakkarfar girgizar ƙasa taa yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutane 600 a ƙasar Morocco.

Al’amarin ya faru a daren Juma’a da misalin ƙarfe 11:11pm na dare.

Mahukunta a ƙasar sun ce wannan ce girgizar ƙasa mafi ƙarfi da aka taɓa yi a cikin ƙasar.

Hanyoyin sadarwa sun katse na tsawon mintuna goma sai daga bisani su ka koma aiki.

Ministan harkokin cikin gidaa a ƙasar ya bayyana aa yau asabar cewa mutanen da su ka mutu sun kai su 632 kuma fiye da rabi sun mutu ne a yankunan Al-Haouz da Taroudant Province.

Sauran wuraren da laamarin ya shafa sun haɗa da Chichaoua, Azilal, Youssoufia provinces, Marrakesh, Agadir da Casablanca.

Ministan ya ce mutane 329 ne su ka jikkata a snadin girgizar ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: