Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗaɗe har dala miliyan 163 daga bankin raya nahiyar Afrika (AfDB), domin bunƙasa noman alkama.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a fadar mai martaba sarkin Argungu Alhaji Sumaila Muhammad.

Shettima wanda ya je Argungu domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu wajen ta’aziyyar fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Giro Argungu da ya rasu a makon da ya gabata.
Ya bayyana cewa yanzu haka gwamnati ta riga da ta karbo bashin dala miliyan 163 daga bankin na AfDB, kuma nan ba da jimawa ba za a kaddamar da shirin haɓaka noman na Alkama.

Shettima ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta cika duk alƙawuran da ta ɗauka musamman ma a bangaren noma domin samar da abinci.
A yayin da ya ziyarci gidan marigayi Giro Argungu, Shettima ya bayyana cewa Najeriya da ma Afrika baki ɗaya sun yi babban rashi na fitaccen malamin addinin Musulunci.