Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ma’akatan lafiya dubu 400 da ake da sun kasar sun yi kadan.

Ministan lafiya da walwalar Jama a Ali Pate ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Ali Pate yayi bayani akan cewa akalla ma’akatan lafiya dubu 400 da ke Najeriya sun yi kadan a kasar.

Ya ce adadin ma’aikatan lafiya dubu 400 sun hada da likitoci da ungozoma da masu taimaka musu da sauran wadanda ke da jibi a da harkar lafiyar.
Ministan Pate ya ci gaba da cewa hakan nakasu ne a bagaren kafiya.
Ya ce duba da akalla Najeriya yan Najeriya akwai mutanen kimanin miliyan 220.
Ya ce hakan ba zai I sa ba ga yan Najeriya a bangaren.
Ko a labaran da muka kawo muku na asubahin wannan Rana gun ji cewa kungiyar likitoci ta kasa ta ce likitoci sama da 500 ne suka bar kasa Najeriya zuwa kasar waje yin aiki.