A wani labarin ma wani kwale-kwale da ke dauke da fasinjoji yayi hadari a garin Guri da ke cikin karamar Hukumar Fufore ta Jihar Adamawa.

Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa a Jihar Dr Muhammad Suleiman ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
Suleiman ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da tsakar ranar Litinin a lokacin da mutanen suka cika jirgin.

Sakataren ya ce bayan samun labarin faruwar lamarin suka aike da jami’ansu gurin domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wata majiya a Jihar ta tabbatar da cewa mafi yawan wadanda lamarin ya rutsa da su mata ne da kananan yara, a lokacin da suke dawowa gida daga gonakinsu wasu kuma daga gurin taron suna.
Amma hukumar bata bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba da wadanda suka jikkata.
A ‘yan makonnin nan an samu yawaitar kifewar jirgin na kwale-kwale a wasu Johohin Najeriya, wanda hakan yake haifar da asarar rayukan mutane wasu kuma su jikkata.