Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bayar da umarni fara baiwa sabbin malaman makaranta horo a jihar.

Gwamnatin ta ɗauki malamai 7,325 tare da sanya mako guda domin fara basu horo.

Gwamnan ya ce bayan kammala samun horon za a basu takardar ɗaukar aiki.

Gwamnan ya bayyana haka yayin da ya ke karbar kwamitin shirya jarrabawar daukar sabbin malaman.

Shugaban kwamitin Dakta Dahiru Yusuf ya ce an raba malaman kashi daban-daban wasu za su koyar da daliban firamare wasu su koyar da na sakadire da kuma wadanda zaa su koyar na takaitattun lokuta.

Ya ce malamai 7,325 ne su ka samu nasara daaga cikin mutane 7,762 da su ka nemi aikin.

Gwamnan ya nuna jin dadinsa ganin yadda ya kama hanya don ganin ya cika alƙawarin da ya ɗauka a ɓangaren ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: