
Ƴan Sanda A Katsina Sun Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kashe Kwamishinan Ƴan Sanda a Katsina yayin musayar wuta.
An kashe Aminu Umar a watan Juli na shekarar 2022.

Rundunar yan sanda a jihar Katsina sun kama wani Sa’idu Yaro da ake zargi da hannu cikin waɗanda su ka hallaka mataimakin kwamishinan yan sanda.

An hallaka Aminu Umar da wani jami’in ɗan sanda kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Haka na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar kuma ya aikewa da Matashiya TV.
Ya ce ana zargin Sa’idu Yaro wanda ya daɗe ana nema ruwa a jallo bayna zargin haɗa kai da aikata muggan laifuka a jihar.
Daga cikin laifin da ake zarginsa da aikatawa har da kisan babban jami’in ɗan sanda a jihar.
A cikin sanarwar da ke nuna ayyukan rundunar da nasarorin da ta samu, kakakin ƴan sandan ASP Abubakar Sadiq ya ce sun samu nasarar kama mai kaiwa yan bindiga bayanai, da kuma kwato harsashi mai yawa daga wajensa.
Haka kuma akwai wani Saminu Usman mai shekaru 19 a duniya, wanda aka kama bayna zarginsa da yin garkuwa da wani yaro mai shekaru biyar a duniya.
Rundunar ta ce su na ci gaba da bincike a kan mutanen da ake zargi, yayin da wasu tuni su ka amsa laifunsu.