Connect with us

Siyasa

Kwamishina Yayi Barazana Ga Alkalai, Da Yunkurin Tayar Da Tarzoma A Kano

Published

on

Kwamishinan kula da kasa a jihar Kano Adamu Aliyu Kibiya, ya yi barazana ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamna.

Sannan kuma ya yi alkawarin tayar da rikici ga mazauna jihar, fiye da rikicin da al’ummar makotan jihar na jihohin Kaduna da Zamfara su ke fuskanta.

Mazaunan jihohin Kaduna da Zamfara dai su na fuskantar tashin hankalin hare-hare, kisa, da kuma garkuwa da su don karbar kudin fansa daga ‘yan bindiga.Wannan hare-haren dai yana faruwa sama da shekaru 10.

Aliyu ya yi zargin cewa, da akwai yiwuwar an bai wa alkalan cin hanci da rashawa dan su yi hukuncin da ba zai yi wa jam’iyyarsa dadi ba.

Kwamishinan ya yi barzanar cewa, idan alkalan kotun su ka yi hukuncin da bai bai’wa jam’iyyarsa ta NNPP nasara ba a korafin dake gabanta, to zasu biya bashin hakan da rayuwarsu.

Jam’iyyar APC da dan takarar gwamnanta Nasiru Yusuf Gawuna dai, su na kalubalantar nasarar da gwamnan jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf ya samu a zaben da ya gabata.

Kotun sauraron kararrakin zaben dai har yanzu ba ta sanya ranar da za ta yanke hukunci a kan shari’ar ba, yayin da Aliyu Adamu ya yi wannan ikirarin lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar NNPP yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a ranar Alhamis.

Taron da aka gudanar kuma ya hadar da yin addu’a, don fatan yin nasara ga tsagin nasu a hukuncin da za a yanke.

Click to comment

Leave a Reply

Siyasa

Jam’iyyar APC Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Almundahanar Kuɗaɗe

Published

on

Jam’iyyar APC da gwamnatin jihar Kano sun yi musayar yawu kan zargin wani shiri na karkatar da sama da Naira biliyan Takwas na kuɗin ƙananan hukumomin jihar.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin karkatar da naira biliyan 8,080,190,875.13.

A cewarsa rashin tabbas kan abin da zai kasance sakamakon hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan zaɓen gwamnan jihar ya sanya gwamnatin ɗaukar wannan matakin.

Shugaban jam’iyyar APC ya kuma gargadi ƙananan hukumomi da bankunan kasuwanci da su dakatar da shirin fitar da kuɗaɗen.

Jaridar Daily Trust ta ce da yake mayar da martani, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bayyana cewa.

Sannen abu ne cewa gwamnatin jihar Kano a ƙarƙashin ingantaccen shugabancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, a cikin watanni bakwai da suka gabata ta yi suna wajen ganin an tabbatar da gaskiya da adalci da amfani da dukiyar al’umma yadda ya dace.

Ya kara da cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba za ta bari mutanen da ke jin zafi ba domin faɗuwa zaɓe kaɗai ba, amma saboda sun yi asarar hanyoyin satar dukiyar gwamnati su ɗauke mata hankali ba.

Continue Reading

Siyasa

Allah Ya Zaɓa Wa Al’ummar Kano Mafi Alheri A Kotun Ƙoli – Sanata Shekarau

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya tofa albarkacin bakinsa game da shari’ar zaben da ake yi a kotun koli.

A wata zantawa da aka yi da shi, Sanata Ibrahim Shekarau ya ba gwamna Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna shawara.

Babban ‘dan siyasar ya yi kira ga gwamna mai-ci da Nasiru Yusuf Gawuna da kotu ta ce shi ya lashe zabe da su koma Allah SWT.

Malam Shekarau ya bukaci ‘yan siyasar su roki zabin Ubangiji kuma su karbi duk kaddarar da ta auka masu bayan hukuncin kotu.

Rohoton na zuwa ne a daidai lokacin da ake jiran kotun koli ta yi hukunci karshe a shari’ar zaben gwamnan na jihar Kano.

Tsohon Ministan ilmin ya yi magana a Rumfar Afrika, ya ce abin da ya fi dacewa shi ne ayi addu’ar zabi mafi alheri ga mutanen Kano.

Shekarau wanda ya yi gwamna tsakanin shekarar 2003 da 2011 ya yi wannan addu’ar, sannan ya ce yana fatan APC da NNPP za su yi irin haka.

 

Continue Reading

Siyasa

Muna Da Ƙwarin Guiwar Samun Nasara A Kotun Ƙoli – Abba Kabir Yusuf

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana kwarin gwiwarsa a game da hukuncin Kotun Koli.

Abba Kabir ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 24 ga watan Disamba a filin wasa na Sani Abacha yayin bikin horas da matasa 2,500 a jihar.

Gwamnan ya yabawa alkalan kan yadda suka dage don ganin sun yi adalci kan shari’ar da ke gabansu.

Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu da kuma kara musu karfin gwiwa kan alkalan kotun.

Abba Kabir ya tabbatar wa magoya bayansa cewa ya na da tabbacin samun nasara a shari’ar da za a yanke.

Wannan na zuwa ne bayan da kotunan baya su ka soke nasararsa.

Gwamnan ya sake daukaka kara zuwa Kotun Koli inda a ranar Alhamis 21 ga watan Disamba ta zauna domin sauraron korafin

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: