Connect with us

Labarai

Kungiyar Ma’aikatan Kwalejin Fasaha A Kaduna Ta Bai Wa Gwamnati Mako Guda Ta Shawo Matsalar Tsaro

Published

on

Kungiyar malamai da ma’aikatan kwalejin fasaha mallakin jihar Kaduna ta Nuhu Bamalli, ta bayar da tsawon mako guda a matsayin wa’adi na karshe ga gwamnatin jihar ta Kaduna, da ta shawo kan matsalar tsaro da kuma tabarbarewar tsarin koyo da koyarwa a kwalejin.

 

A wani tsari na hadakar ganawa da manema labarai da kungiyoyin biyu suka gudanar a Zaria ranar Lahadi, shugaban kungiyar malamai ta kwalejin Usman Shehu Sulaiman ya ce, ma’aikatan za su tsunduma yajin aiki idan har gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu.

 

Usman ya ce a ranar 11 ga watan Yuni na shekarar 2021, an yi garkuwa da malaman makarantar, iyalansu, da wasu dalibai.

 

Hakan ya sanya gwamnati ta maye gurbin jami’an tsaron makarantar da sojoji da kuma wasu daga cikin kungiyar bayar da tsaro ta jihar Kaduna.

 

Ya kuma bayyana cewa, sojoji da jami’an tsaron da suke aiki a kwalejin suna tunanin barin aikin, sakamakon rashin biyansu hakkokinsu.

 

Ya kuma ce janyewar jami’an tsaron zai sanya kowa cikin hatsarin sacewa da sauran ayyukan laifi.

 

Ya kuma ce kudaden da ake bai wa kwalejin duk wata ba a basu ba tun watan Fabarairu, hakan ya janyo makarantar ta dage gudanar da jarrabawa da kuma sakin sakamakon jarrabawa, da kuma samar da katin shaida ga daliban makarantar.

 

A nasa bangaren shugaban kungiyar ma’aikatan kwalejin da ba masu koyarwa ba, Mahmud Aliyu Kwarbai ya bayyana cewa, ‘yan kungiyarsu suna rayuwa cikin tsananin tsoron rashin tsaro.

 

Jami’in hulda da jama’a na kwalejin Abdullahi Shehu ya shaida wa ‘yan jaridu cewa, hukumomin makarantar suna iya kokarinsu dan ganin sun biya bukatun kungiyoyin.

 

 

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Tinubu Ba Zai Sauka Daga Manufofin Da Ya Ke Kai Ba – APC

Published

on

Jam’iyyar APC a Najeriya ta ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai jingine kudirin da ya dauka na gyaran kasa tare da komawa baya ba.

A cewar jam’iyyar matakin da shugaban ke ɗauka hanya ce don kawo sauyi da cigaba ga ƙasar.

Sannan jam’iyyar ta musanta zargin yin magudi a yayin zaben da aka yi a Jihar Edo.

A sakon da jam’iyyar APC ta fitar a yau wnda ke zama martani ga jam’iyyar PDP, daraktan yada labarai na jam’iyyar Alhaji Bala Ibrahim ya ce jam’iyyar ba ta da nufin sauka daga turbar demokaradiyya.

Ya ce tsari da manufofin da jam’iyyar ta saka a gaba asara ce kuma ci gaba ne ga ƙasar.

Haka kuma tsarin da su ke kai ba zai tauye demokaradiyya ba.

Continue Reading

Labarai

Kotu A Ekiti Ta Yanke Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Masu Aikata Fashi Da Makami

Published

on

Babbar kotu a jihar Ekiti ta yanke hukuncin kan wasu mutane uku da ake samu da aikata fashi da makami.

 

Kotun a jiya Laraba ta yankewa mutanen hukuncin kisa ta hanyar rataya.

 

Wadanda aka samu da laifin sun hada da Alexander Solomon , da Desmond Peter sai Eric Tile.

 

Kotun ta sallami cikon na hudun da aka zarga Promisr Shir bayan da aka gani ba shi da hannu a ciki

 

Wadanda aka yankewa hukuncin an samesu ne da laifukan fashi da makami, mallakar makaami ba bisa kaida ba da kuma kisan kai.

 

Wanda da aka yankewa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2022 a tsakanin Illumoba-Aisegba da ke kan titin Ekiti zuwa Aisepba Ekiti.

 

A wajen ne kuma su ka yi fashin naura mai kwakwalwa ta tafi da gisanka, da kudi naira 540,000 wayoyin hannu da sauransu.

 

Saannan su ka yi kisan kai

 

Bayan gabatarwa da kotun hujjoji ne kuma kotun ta gamsu tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya

Continue Reading

Labarai

Majalisar Dattawa Na Shirin Yiwa Kundin Tsarin Mulkin Kasar Kwaskwarima

Published

on

Majalisa dokoki a Najeriya na shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima bayan da kotun koli ta bai wa kananan hukumomi yancin gashin kansu.

 

Majalisar ta ce za ta yi gyaran ne don sake jaddada hukuncin kotun koli da ta bai wa kananan hukumomin dama.

 

Kudirin ya fito daga mataimakin shugaban majalisar Barau I Jibril kumaa ya samu goyon bayan Sanata Abdul Ningi fa Sanata Tahir Monguno.

 

Daga cikin hukuncin da kotun ta yi ta umarci a tura kason kananan hukumomin kai tsaye zuwa asusunsun, maimakon hadaka da asusun jiha da ake yi a baya.

 

Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya jaddada cewar, majalisar na goyon bayan hukuncin da kotun kolin ta yi, ya ce za su yi aiki a kundin tsarin mulkin domin ganin an shigar da dokar a ciki.

 

A ranar 11 ga watan Agusta ne dai kotun koli a Najeriya ta yanke hukunci damgane da bai waa kananan hukumomi yancin gashin kansu.

 

Wanda kotun ta ce daga lokacin gwamnatin tarayyaa ta dinga aike da kudadensu kai tsaye ga asusunsu.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: