Shugaban ma’aikata na jihar Lagos, Hakeem Muri Okunola, ya aike da takardar sauka daga mukaminsa domin tunkarar sabon mukamin da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shi na Sakatare na musamman ga shugaban kasar.

 

A wata takarda ta ajiye aikin da ya sanya wa hannu, shugaban ma’aikatan na jihar Lagos ya bayyana cewa ajiyewar za ta fara ne daga ranar 29 ga watan Satumba da muke ciki.

 

Hakeem ya tabbatar da cewa ya sanar da gwamnan jihar ta Lagos Babajide Sanwo-Olu kan wannan ajiye aiki na kashin kai bayan shafe shekaru biyar yana rike da ofishin na shugaban ma’aikata.

 

Ya godewa gwamnan jihar da hukumomi da ma’aikatu da yan majalisar zartarwa da sakatarorin dindindin da daukacin ma’aikatan jihar Lagos kan irin hadin kai da goyon baya da suka ba shi.

 

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai fadar shugaban kasa ta bayyana nadin sakataren inda ta bukace shi da yayi amfani da kwarewarsa don yin aiki da zai tabbatar da nasara.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: