Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi ta ayya Dakta Bala Muhammad a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Kotun ta ayyana Dakta Bala a yau bayan da ta kammala sauraron korafin kowacce jam’iyya a da su ke kalubalantar nasararsa.
Kotun ta yi watsi da bukatar da take kalubalantar nasarar daga jam’iyyar adawa.
An shigar da korafin a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar bayan ayyanashi da hukumar zabe ta kasa INEC ta yi a watan Maris.

Dakta Bala Muhammad ya kasance gwamna jihar a karo na biyu bayan da ya sake lashe zabe a zaben da ya gabata.

Daga karshe kotun ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta wanda ake kalubalantar nasarar Dakta Bala.