Tsohon dan takarar gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya sha alwashin yi wa yan jihar Kano adalci a cikin mulkinsa.

Dakta Gawuna ya bayyana haka a wata hira da BBC bayan da kotu ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar a shekarar da mu ke ciki.
A jawabinsa ya ce tun da farko ba su yi gaggawa don ganin sun mulki jihar ba, sai dai ya ce neman haƙƙi a kotu ba laifi ba ne.

Sannan ya ce ya yi farin ciki da aka ayyanashi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, wanda ya ce hakan babbar nasara ce a gareshi.

Nasiru Gawuna ya abinda kotu ta sanar shi ne haƙiƙanin abinda jama’ar Kano su ke fata, kuma abinda su ke jira kenan.
A cikin jawabin nasa ya sha alwashin yin mulki cikin adalci domin ci gaban jihar.
Idan ba a manta ba, Gawuna ya bayyana a yayin yaƙin neman zaɓensa cewar, zai bai wa ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu muddin ya zama gwamna a Kano.