Gwamnatin tarayya ta sanar da ƙara albashin malaman jami’a a Najeriya.

Gwamnatin ta yi ƙarin ne ta hannun hukumar kula da albashin ma’aikata ta ƙasa tare da amincewa da ƙarin.
Ƙarin albashin ya shafi ƙananan ma’aikata da SU KA SAMU ƘARIN KASHI 25.5%.

Yayin da manyan malaman makarantar da su ka kai matsayin farfesa za su samu ƙarin albashin da kashi 35% na albashinsu.

Wata majiya daga ma’aikatar ilimi ta shaidawa jaridar Punch cewar, an yi ƙarin ne ba tare da sanin ƙungiyoyin malaman ba..
Ministan ilimi a Najeriya Farfesa Tahir Mamman ne ya bayar da umarnin gabatar da tsarin ga hukumar kula da albashin ma’aikata ta ƙasa.
A wani labarin kuma ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU sun ce ba su da masaniya dangane da ƙarin albashi da gwamnatin tarayya ta ce ta yi.
Farfesa Emmanuel Osodoke da ke zama shugaban ƙungiyar ne ya shaida haka yau yayin ganawa da manema labarai.