Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewar wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ɗaliban jami’a a Gusau babban birnin jihar.

Ɗaliban na karatu ne a jami’ar tarayya ta Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Lamarin ya faru a yau Juma’a kuma ake zargi mafi yawa daga cikin ɗaliban da aka yi garkuwa da su mata ne.

Wani mai suna Abubakar Sani ya shaida cewar an yi garkuwa da ɗaliban a gidan kwanansu da ke ƙauyen Sabon Gida.

Ya ce ƴan bindigan sun shiga ƙauyen ne tare da zagaye gidan ɗauke da makamai, kuma su na da yawa yayin da su ka kai harin.

Abubakar Sani ya ce ƴan bindigan sun yi garkuwa da iya ɗaliban ne kaɗai ba tare da sun yi garkuwa da ko da guda cikin mutanen ƙauyen ba.

Da zuwansu sun fara harbin iska lamain da ake zargi wasu daga cikin ɗaliban sun tsere cikin daji domin tsira.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: