Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta gano haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba na taka rawa wajen ƙaruwar ta’addanci a jihar.

Gwamnan ya bayar da umarnin ɗaukar tsauraran matakai ga duk waɗanda su ka yi burus da dokar hana haƙar ma’adanai ba bsia aƙa’ida ba a jihar.
Gwamnatin ta haramta haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a jihar biyo bayan ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya sanyawa hannu yau Asabar, sanarwar ta ce an ɗauki matakin haka ne domin kare al’ummar jihar.

Haka kuma wannan wani ɓangare ne don ganin albarkatun jihar sun koma ƙarƙashin ikon gwamnati.
Idan ba a manta ba, ayyukan ta’addanci sun ƙaru ko da a jiya Juma’a sai da aka sace wasu ɗalibai na jami’ar tarayya ta Gusau, ko da yake jami’an soji sun ceto shida daga cikinsu.