Rundunar ƴan sanda a jihar Taraba ta ce ta kama wasu mutane 20 da take zargi da yin garkuwa da mutane.

Nasarar na zuwa ne bayan tattara bayanan sirri da aka yi bayan karɓar ƙorafin jama’a dangane da garkuwa da mutane da ake yawan samu a ɓangare daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Abdullahi Usman ya ce waɗanda aka kama sun amsa laifinsu.

Ya ce sun kama bindigu ƙirar AK47 guda uku da kuma wata bindiga daban.

Sannan ya ce mutanen da ake zargi sun karɓi kuɗi sama da naira miliyan 30 daga ƴan uwan waɗanda su ka yi garkuwa da su.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ya ce rundunar ba za ta gaza ba wajen farautar mutanen da ke aikata laifuka a jihar.
Sannan za su ci gaba da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.