Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu ma’aikata da ke aikin wani gini a jami’ar tarayya ta Gusau a jihar Zamfara.

Mutanen sun ne ɗakin kwanan ma’aikatan haye kan babura sannan su ka umarcesu da su bisu su tafi.
Wani da ya sha da ƙyar wajen mutanen mai suna Ibrahim Muhammad ya ce da zuwansu su ka ɓalle ƙofa sai dai ya stammu tsallakawa ta taga sannan ya tsere..

Ya ci gaba da cewa yunƙurinsa ke da wuya na tsallakewa ƴan bindigan su ka buɗe masa wuta sai dai ba su sameshi ba.

Lamarin ya faru a ranar Juma’a bayan da aka samu labarin wasu ƴan bindiga da su ka yi garkuwa da wasu ɗaliban jami’ar tarayyar ta Gusau.
Jaridar Punch da ta samo labarin ta ce ta yi duk mai yuwuwa domin ji daga bakin mahukuntab a makarantar amma ba su magantu a kai ba.
Ma’aikatan da ake zargi an sace sun kai su Tara, yayin da aka yi garkuwa da ɗalibai da dama wanda mafi yawa daga ciki mata ne duka a ranar Juma’a.