Gwamnatin Najeriya ta magantu dangane da zargin da gwamna Zamfara Dauda Lawal Dare ya yi na sulhu da ƴan bindiga a jiharsa.

Ministan tsaro a Najeriya Badaru Abubakar ne ya ce sam gwamnatin ba ta wani shirin yin sulhu da ƴan bindiga kamar yadda gwamnan ya yi zargi.

Gwamnatin ta musanta zargin ne a yau bayan da gwamnan Zamfara ya zargesu da yin sulhu kuma hakan na iya zama mayar da Hakan na zuwa ne bayan da aka yi garkuwa da wasu ɗalibai na jami’ar tarayya ta Gusau a jihar a makon jiya.

Gwamnatin ƙasar ta ce ba ta sanya wata ƙungiya ko hukuma tattaunawa da ƴan bindiga ba, a don haka zargin ba gaskiya ba ne.

Sannan gwamnatin ta himmatu wajen kuɓutar da ɗaliban da aka sace, kuma ana samun kyakkyawans akamako.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta ƙsar Attari Hope ya ce shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni domin ganin an samar da kyakkawan sakamako wajen ceto ɗaliban.

One thought on “Ba Mu Tura Kowa Ba Ya Gana Da ‘Yan Bindiga A Zamfara – Badaru Abubakar”

Leave a Reply

%d bloggers like this: