Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun sanar da ranar 3 ga watan Oktoba mai kamawa a matsayin ranar da za a shiga yajin aikin gama gari.

Wannan yajin aiki da za a shiga ya sha bamban da wanda aka yi a baya na gargaɗi a kan halin matsin rayuwa da ake ciki a Najeriya.
Shugabannin ƙungiyoyin NLC da TUC ne su ka sanar da haka, bayan wani zama da su ka yi a yau domin yanke matsaya a dangane da yajin aikin da za su tafi.

Yajin aikin da za a shia, zai shafi dukkanin ma’aikatun da ke ƙarƙashin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC na dukkanin jihohin Najeriya har da Abuja.

A cewar ƙungiyoyin, ba su ga wani sauyi ba bayan da su ka yi yajin aikin gargaɗi tare da zanga-zanga a baya kan tsadar mai da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
Ƙungiyoyin sun yanke shiga yajin aikin domin tabbatar da samun muradinsu, wanda su ka shimfiɗawa gwamnatin wasu sharruɗa kan cire tallafin man fetur.
Dangane da shirin tafiya yajin aikin da ƙungiyoyin za su yi, gwamnatin tarayyar ƙasar ta roƙesu da su dakatar da shiga yajin aikin.
Channels TV ta ruwaito yadda ministan ƙwadago a Najeriya Simon Lalong ke roƙon ƙungoyin da su dakatar da shirinsu na tafiya yajin aikin da su ke ƙoƙarin farawa a wata mai kamawa.