Babban sufeton yan sandan Najeriya ya bayyana takaicinsa matuka kan hare-haren da ake Kai wa yan sandan kasar.

Shugabar ya bayar da umarni kan irin wadannan hare-haren don a zaluko wadanda suke aikata hakan kuma a hukuntasu kamar yadda doka ta tanadar.


Ya Kuma Kara da cewa a kwanakin nan an kai wa wani baturen yan sanda hari har gurin aikinsa tare da hallaka shi.
Sakamakon iren iren hare-haren, jami’in ya bayar da umarni ga dukkanin kwamishinonin yan sanda da kuma masu ruwa da tsaki wadanda alhakin Kula da kuma tura yan sanda aiki da su tashi tsaye don ganin an yi bincike kan ire-iren wadannan korafin.