Wasu da ake zargin yan garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da mutane akalla 31 a jihar Naija.

Kamar yadda aka rawaito yan garkuwa sun sace mutane akalla 31 a karamar hukumar Munya ta jihar Naija.


Yan bindigar sun shiga kauyukan Zagzaga da kuma Kabula cikin dare a ranar Alhamis.
Wani shaida da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa yan garkuwa sun je kauyen Zagzaga da yawansu dalilin da yasa da mazajen garin na Zagzaga suka gudu aka sace matansu takawas.
Sannan yan garkuwa sun isa kauyen Kabula tare sace mutane 23 a garin.
Wannan harin na zuwa ne bayan da yan bindigar su ka kai wani hari tare baza mutanen garuruwan.
Sai dai a furucinsa sanata Sani Musa ya bayyana rokonsa ga gwamnatin data kawo dauki a yankunan da yan bindigar suka addaba.