Ministan birnin tarayya Abuja Nysom Wike ya tabbatar da cewa babu gudu babu ja da baya akan ayyukan da ya kuduri aniyar yiwa birnin.

Wike ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja, yayin da yake mayar da martani ga ma’aikatan kamfanin sufuri na AUMTCO wadanda suka koka akan tsige manajan daraktan kamfanin.


Ministan ya bayyana cewa ya na yin hakan ne domin al’ummar birnin na Abuja dama al’ummar Najeriya.
Wike ya kara da cewa ba zai taba gazawa ba wajen ganin ya aiwatar da abinda ya kuduri aniyar aiwatarwa a birnin na Abuja da kewayanta.
Sannan ya ce za su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin birnin na Abuja ya zama cikin tsari, tare da tsige duk wani mai mukami da yake shirin yin almundahana akan aikinsa.
Manajan kamfanin na daya daga cikin shugabannin hukumomi da kamfanonin ma’aikatun gwamnatin tarayya 21 da ministan ya sallama daga bakin aiki a ranar Laraba.