Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin sai baba-ta-gani da za a tafi ranar 3 ga Oktoba, 2023 bayan cire tallafin man fetur.

Idan dai za a iya tunawa, kungiyar kwadago ta Najeriya ta umurci gamayyar kungiyoyin ta a fadin kasar da su tashi tsaye tare da rufe kasar sakamakon kin bin wasu matakai bakwai da NLC da TUC suka gabatar na rage wahalhalun da mutane ke fusakan ta da kasa baki daya.

Hakazalika, shugaban kungiyar ma’aikatan ruwa ta kasa (MWUN) Kwamared (Prince) Dr. Adewale Adeyanju fnli HFCPSP, ya kuma bayar da umarnin a rufe dukkan tashoshin jiragen ruwa na kasar nan, jiragen ruwa, tashoshin mai da iskar gas da kuma tashoshi na kasa.

Sai dai bayan taron gaggawar da aka kira yau 2 ga watan Oktoba 2023 tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago, NLC da TUC sun amince tare da dakatar da yajin aikin domin samun damar aiwatar da bukatun kungiyar ta NLC.

Don haka, majalisar zartaswar NLC ta kasa ta bayar da umarnin cewa dukkan mambobinta da su umarci mambobinsu da su koma bakin aiki a gobe 3 ga Oktoba, 2023 saboda an dakatar da yajin aikin da aka shirya yi.

Kwamared Adeyanju, Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya Kwamared Adeyanju, ya kuma ba da umarnin cewa dukkan ma’aikatan ruwa da su koma bakin aiki gobe kamar yadda kungiyar kwadago ta Najeriya ta umarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: