Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na bakin kokarinsa na ganin an daina maganar shiga yajin-aikin da sai baba-ta-gani a kasar nan.

Sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasar cewa an amince ayi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya karin N10, 000 kan alawus din da za a raba.
Da farko an ji labari N25, 000 da shugaba Bola Tinubu ya yi magana a kai za ta shafi duk wani ma’aikaci, akasin jawabin ranar bikin ‘yancin kai.

A safiyar Litinin kuma sai aka sake fitar da sanarwar kara adadin alawus din daga N25, 000 zuwa N35, 000 da za a biya na watanni
shida.

Daily Trust ta ce da alama kungiyoyin kwadago ba su yi na’am da tayin nan da aka zo da shi ba.
Wata majiya ta shaida cewa ma’aikatan kasar nan a karkashin NLC da TUC sun fadawa wakilan gwamnatin tarayya duk abin da su ke bukata.
Gwamnatin tarayya ta ce tayi karin ne duba da tattaunawar da ake yi da ma’aikata a dalilin tashin farashin man fetur a sakamakon cire tallafi.